Gwamnatin Botswana ta sanar da cewa shugaban kasar Mok-gweetsi Masisi ya harbu da cutar Covid 19.
Kasar Botswana da Afrika ta Kudu sun kasance kasashe biyu da aka fara gano sabon nau’in cutar Korona na Omicron.
Yayinda wasu kasashen Afrika ke iya kokarin ganin jama’ar su sun karbi allurar rigakafin cutar Covid 19, bulluwar sabon nau’in cutar Omicron ya dada saka jama’a cikin shakku.
A Afrika ta Kudu da wasu kasashen daban, hukumomi tare da hadin gwiwar jami’an kiwon lafiya na iya kokarin ganin an takaita adadin masu kamuwa da wannan cuta.
A Botswana yan lokuta da sanar da cewa shugaban kasar ya kamu da kwayar cutar, jami’an gwamnatin sun ce shugaban kasar ta su baya cikin mummunan yanayi, kuma jikinsa bai nuna yana dauke da wannan cuta ba, mataimakinsa ne zai ci gaba da gudanar da harakokin gwamnati.
Daga: RFI Hausa