Shugaban Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Kudu (Federal Medical Center, Birnin Kudu), Dr. Adamu Abdullahi Atterwahmie ya ziyarci Fadar Mai Girma Sarkin Kudu, Alhaji Garba Hassan Jibrin domin ganawa da al’ummar Birnin Kudu.
A lokacin ziyarar, Sarkin Kudu tare da wasu daga al’ummar Birnin Kudu karkashin Kungiyar Muryar Birnin Kudu, sun tarbi Dr. Atterwahmie inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi cigaban FMC Birnin Kudu.
KU KARANTA: Buhari Ya Nada Atterwahmie Shugabancin FMC Birnin Kudu
Da yake jawabi a lokacin ganawar, Dr. Atterwahmie ya ce ya je Fadar Birnin Kudun ne domin ya nuna jin dadinsa bisa tarba da aka yi masa lokacin da aka nadashi Shugaban asibitin.
Ya kuma bayyana cewa, daga zuwansa kawo wannan lokaci, ya samu nasarar aiwatar da aiyukan cigaban asibitin da suka hada da samun waje na din-din-din domin gina rukunin ginin wajen zaman ma’aikatan asibitin a wani waje na musamman da ke wajen asibitin.

Mai Girma Sarkin Kudu, Alhaji Garba Hassan Jibrin, ya nuna jin dadinsa da ziyarar Dr. Atterwahmie, inda yai alkawarin cewa, al’ummar Birnin Kudu za su cigaba da bayar da duk gudunmawa domin ganin cigaban asibitin.
Sarkin Kudu, ya kuma yi kira ga Dr. Atterwahmie da ya samar da Kwamitin Abokai na Asibitin wato Hospital Freinds domin kara samun kusanto da al’ummar Birnin Kudu jikin asibitin da samun cikakkiyar gudunmawarsu wajen cigaban asibitin.
Daga: Kabiru Zubairu