For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shugaban INEC Ya Ce, Ba Za A Iya Yin Maguɗi Ba A Zaɓen 2023

Biyo bayan raɗe-raɗin da ake yi na cewar, masu kutse a intanet zasu yi maguɗin babban zaɓen shekarar 2023, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a jiya Asabar ya ce, hukumar zata yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta kare martabar ƙuri’un mutane.

Farfesa Yakubu ya yi wannan magana ne a jiya da daddare, lokacin cin abincin dare wanda Ƙungiyar Tarayyar Turai, EU, ta shirya.

A wajen cin abincin, wanda aka gabatar a Dandalin Tafawa Balewa da ke Lagos, mawaƙan Najeriya na ƙungiyar Youth Vote Count 2.0 sun sami zarafin tattaunawa da shugabannin hukumar.

Shugabannin INEC da Mawaƙa a Wajen Taron

A wajen taron, Farfesa Mahmood Yakubu, ya jaddada cewa, dukkanin ƴan Najeriya da ba su yanki katin zaɓe ba, kuma suna da buƙatar yin hakan, hukumar zata ba su dama.

Ya kuma kawar da shakkun da ke zuciyar wasu ƴan Najeriya, na cewar wa’adin katin zaɓe yana iya ƙarewa, inda ya ce, katin ba shi da ƙarshen wa’adi.

Da yake kawar da tsoron da wasu ke da shi na zargin yin maguɗi, Shugaban na INEC ya ce, hanya mafi dacewa ta kare martabar ƙuri’a ita ce abin da ke faruwa a rumfunan zaɓe.

Ya ce, babu wani wajen tattara sakamakon zaɓe da ƙirga su da ya wuce rumfar zaɓe.

A rumfar zaɓe ne ake juye ƙuri’u a ƙirga su a kuma shigar da bayanai kan su, sannan kuma a ɗora a shafin hukumar INEC wato INEC Result Viewing Portal (IReV).

Ya ƙara da cewa, wannan ita ce hanya mafi inganci a harkar zaɓe, kuma Najeriya ce ta farko a fara amfani da irin wannan hanyar, wadda zata baiwa ƴan ƙasa damar ganin sakamakon zaɓen mazaɓunsu da zarar an gama zaɓe a rumfuna.

A ƙarshe ya jaddada ƙarfin guiwarsa na cewa INEC zata yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa ba a sami maguɗi ba a babban zaɓen na shekarar 2023.

Comments
Loading...