For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shugaban Jam’iyyar PDP Na Zamfara Ya Rasu

Jam’iyyar Peoples Democratic Party ( PDP) a jihar Zamfara ta tabbatar da rasuwar shugabanta na jihar, Dr. Ahmed Sani Ƙaura.

Sakataren jam’iyyar a jihar, Faruk Ahmed Gusau ya shaida wa BBC cewar, Dr. Sani ya rasu ne bayan ganawa da majalisar malamai ta jihar.

Majalisar ta malaman ta gayyaci shugaban jam’iyyar ne domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar dabanci a lokacin yaƙin neman zaɓen shekara ta 2023 a jihar.

Sai dai jim kaɗan bayan kammala taron ne shugaban jam’iyyar ya faɗi, inda aka garzaya da shi asibiti inda a nan ne aka tabbatar da rasuwar tasa.

Ya rasu yana da shekaru 62 a duniya, ya kuma bar mata biyu da ‘ya’ya 6.

Comments
Loading...