For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shugaban Miyatti Allah Ya Ce Ba Shi Da Wata Alaƙa Da Ta’addanci

Shugaban Miyatti Allah Kautal Hore, Alhaji Bello Bodejo, wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen ta’addanci ya buƙaci kotu da ta bayar da belinsa, inda ya ce ba shi da wani tarihi na aikata ta’addanci.

Bodejo wanda ke fuskantar tuhuma a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya kuma musa cewar yana da hannu wajen samar da ƴansintirin ƙabilar Fulani mai suna Ƙungiyar Zaman Lafiya.

Shugaban na Miyatti Allah wanda aka kama a Karu da ke Jihar Nasarawa ranar 23 ga watan Janairun shekarar nan, ya bayyana hakan ne ta bakin ɗan’uwansa Mohammed Musa, a takardar neman neman beli mai ɗauke da kwanan wata 28 ga Maris, 2024.

Mohammed Musa ya ce, ɗan’uwan nasa ya yi wa kamfanin sintiri ne mai suna Nomad Vigilante Nigeria Limited rijista, wanda ke samar da aiyukan samar da tsaro ga al’umma da kuma bunƙasa zaman lafiya amma ba aiyukan ta’addanci ba.

Sai dai a takardar musa bayar da belin mai dauke da kwanan watan 2 ga Afrilu wadda jami’in Sashin Shigar da Ƙorafe-Ƙorafen Al’umma na Ma’aikatar Shari’a ta Ƙasa, Noma Ganau Wando ya shigar, ya buƙaci kotun da ta yi watsi da neman belin bisa rashin cikakkun hujjojin bayar da belin daga ɓangaren Bodejo.

Comments
Loading...