Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Joe Ajaero, wanda aka kama, an sako shi a daren Litinin da ta gabata daga hannun hukumar tsaro ta DSS, duk da cewa matakin hukumar ya jawo suka daga sassa daban-daban na kasar.
Wani daga cikin shugabannin NLC ya tabbatar wa jaridar Vanguard cewa an sako Ajaero da misalin karfe 11:10 na daren jiya.
An kama Ajaero ne a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayin da yake shirin tafiya London don halartar taron Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC na ƙasar Birtaniya da aka fara jiya, bayan hukumar DSS ta mamaye ofishin kungiyar SERAP saboda zargin yin kira ga gwamnati da ta janye ƙarin farashin man fetur.
SERAP ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya umarci DSS ta dakatar da wannan mataki nata.
Shugaban sashen yada labarai na NLC, Benson Upah, ya tabbatar da kamun Ajaero, amma ya ce kungiyar bata san inda yake ba, yana mai cewa DSS ce ta kama shi.
Rahotanni sun nuna cewa an tura shugaban kwadagon zuwa hukumar leken asiri ta kasa (NIA).
An kama shi ne kwana 11 bayan da ya amsa gayyatar ƴansanda a ranar 29 ga Agusta kuma aka sake shi a wannan rana.