For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shugaban NNPP Na Jihar Kaduna Ya Fice Daga Jam’iyyar

Shugaban Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), na Jihar Kadun, Ben Kure, ya sanar da ajjiye mukaminsa da kuma ficewarsa daga jam’iyyar a jiya Alhamis.

Da yake jawabi ga manema labarai jiya a Kaduna, Ben Kure ya ce, duk da yana matukar mutunta dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Rabi’u Musa Kwankwaso, shi yanzu ba dan jam’iyyar ba ne.

Da yake bayyana dalilin sabun sabaninsa da jam’iyyar, ya ce, jam’iyyar NNPP ba ta da karfi a Jihar Kaduna, inda ya kara da cewa, mutum ba zai zama dan takarar gwamna a jam’iyya ba sannan kuma ya ce shi zai gudanar da jam’iyyar.

Ya kuma ce, mutane da dama sun bar jam’iyyar saboda rashin bayar da dama, inda ya kara da cewa, ya yi iya bakin kokarinsa wajen ciyar da jam’iyyar gaba, duk hukuncinsa na ficewa.

“Ina sanar muku  da sauran magoya bayana da abokan hulda cewa, na sauka daga mukamin shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kaduna, kuma ni yanzu ba dan jam’iyyar ba ne. Zan huta, na yi nazari a kan makomar siyasata sannan na sanar da al’umma a lokacin da ya dace,” in ji shi.

Comments
Loading...