Shugaban Jam’iyyar PDP reshen jihar Jigawa, Babandi Ibrahim ya yi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya fito da bayanin tsarin da za a bi wajen zabo mutum miliyan 40 da za su amfana da tallafin rage radadin cire tallafin mai na Naira 5000.
Shugaban PDP a Jigawan, ya bayyana hakanne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a Dutse yayin gudanar da Ganawa da ‘Yan Jaridu na Sati Sati da ake yi.
Ya bayyana cewa akwai bukatar shugaban kasa ya fadawa ‘yan Najeriya hanyar da tallafin sufurin zai isa ga wadanda aka nufa.
Babandi Ibrahim ya bayyana cewa tsarin gaba daya ba dabara ba ce, inda ya ce “babu wata hanya da hakan zai temaka wajen rage radadin da cire tallafin zai jawo ga talakawa”.
“Cire tallafin mai gaba daya abu ne da zai jefa ‘yan Najeriya da kuma talakawa cikin bakar wahalar rayuwa, baya da wahalar da ake ciki yanzu ta tsadar kayan abinci da ababen more rayuwa da kuma matsalar tsaro.”
Shugaban PDP na Jigawa ya yi kira ga shugaban kasa da ya dakatar da yunkurinsa na cire tallafin, tare da bijiro da tsare-tsaren da za su temaka wajen bunkasa walwalar al’umma ta hanyar samar da aiyukan yi.
A karshe shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta tsara yanda za ta karbi mulki daga jam’iyyar APC a jihar Jigawa a shekarar 2023, inda ya ce dama al’umma sun nuna cewa zun gajiya da APC.