Daga: RFI Hausa
Shugaban sojin Sudan Janar Abdel Fatah al-Burhan ya bayyana sunayen sabbin ‘yan majalisar rikon kwaryar kasar bayan juyin mulkin da ya yi a watan jiya.
Shugaban sojin zai jagoranci majalisar, yayin da Mohammed Hamdan Daglo, shugaban rundunar sojin kai daukin gaggawa zai zama mataimakinsa.
Wannan na zuwa ne makwanni biyu da Burhan ya rusa gwamnatin Firaminista Abdalla Hamdok wanda aka tsare tare da ayyana dokar-ta-baci a fadin kasar.
Kazalika sabon garanbawul din na zuwa ne kwanaki biyu gabanin wata gagarumar zanga-zanga da al’ummar kasar suka shirya gudanarwa domin nuna adawa da juyin mulki. na ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata.