For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shugaban Tunisia, Kais Saied Na Zargin ‘yan Siyasar Faransa Da Yi Masa Katsalandan

Shugaban kasar Tunisia Kais Saied ya zargi wasu ‘yan siyasar Faransa da kitsawa kasarsa manakisa ta hanyar amfani da ‘yanciraninta da ke ketare musamman wadanda ke Faransa.

A wani jawabinsa karon farko gaban Majalisar Tunisia, Kais Saied ya ce Tunisia kasa ce mai cikakken ‘yanci da bata bukatar a yi mata katsalandan a harkokinta daga waje.

Kais wanda bai kama sunan wadanda ya ke zargi da kitsawa kasar manakisa ba, ya ce ‘yan siyasar kasar da ke ketare su na amfani da ‘yan ciranin Tunisa wajen caccakar manufofin Tunisia.

Ana ganin Kalaman na Kais Saied a matsayin shagube kan magabacinsa Moncef Marzouki da a baya-bayan nan ya kwatanta salon kamun ludayin Kais da yunkurin juyin mulki.

Marzouki wanda ya shugabancin Tunisia daga shekarar 2011 zuwa 2014 yayin wani jawabinsa gaban masu zanga-zangar adawa da Kais Saied a birnin Paris, ya bukaci Faransa ta yi fatali da duk wata bukata da Tunisa ta shigar mata.

Sai dai shugaban na Tunisia wanda a farkon makon nan ya kafa majalisarsa bayan rusheta a baya, ya caccaki kalaman na Marzouki tare da bayyana shi a matsayin maci amanar kasa.

Comments
Loading...