Sanannen malamin addinini Musulunci, Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu ya bayyana cewa dole ne a kowanne hali al’umma su zama suna da shugabannin da za su shugabance su.
Ya bayyana hakan ne a taron taya murna da tunasar da shugaban karamar hukumar Birnin Kudu da ke jihar Jigawa, Hon. Magaji Yusuf Gigo da ‘yan majalissarsa.
Kungiyar cigaban karamar hukumar Birnin Kudu ta Birnin Kudu Progressive Forum (BPF) ce da shirya taron a dakin taro na Da’u Aliyu Hall da ke garin Birnin Kudu.
A yayin gabatar da jawabinsa, babban bako mai jawabi, Dr. Abubakar Sani Birnin Kudu ya ce; “Shugabanci ba na dolo ba ne, wanda ya ke ba shi da basira tasa ta kansa sai dai wadansu su zo su gara shi, a ce masa yi kaza, yau wannan ya zo masa da wannan shawara, sai ya karkata, washe gari wani ya zo ya ce ai kaza ya kamata, shi ma sai ya ce dawo nan, in an jima wani in ya zo shima sai yua kada shi nan – ba a son haka a shugabanci.”
Ya ce ana son shugaba “mai tsayuwa da jajircewa a kan shugabanci. In an ce tsayuwa da jajircewa ba ya nufin ka taka mutane, ka rena kowa, ba mai hankali sai kai – wannan ba a son haka.”
“Ku duba Manzon Allah S.A.W mana, wanda shine babban abin koyinmu, babu wanda ya kai shi iya shugabanci – amma ba mai tsattsauran ra’ayi ba ne. Shugabanci ba na mai tsattsauran ra’ayi ba ne a kowanne fanni.”
“Shi danadam shi kadai ba zai kammala ba, in akwai mai kammala a ‘yanadam to Manzon Allah ne S.A.W, amma duk da haka, duk da kamalar dan’adamtakar Manzon Allah S.A.W sai da Allah ya umarce shi ya shawarci Sahabbai”.
“Bayan karfin mulki to kuma a hada shi da ilimi, da basira da sassauci da kuma girmama mutane. Idan ya zama shugaba mai rena kowa ne to ba za a ci nasara ba.”
Tun a farko taron, shugaban kungiyar BPF, Malam Bala Muhd ya ce sun shirya taron ne don taya murna da kuma zaburar da shugabannin kan kokarin sauke nauyin da yake kan su.
Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Hon. Magaji Yusuf Gigo ya bayyana jin dadinsa ga abubuwan da aka tattauna a taron, tare da godewa kungiyar BPF kan wannan yunkuri.
Shugaban ya ce yana alfahari da wannan lamari kasancewar shine shugaba na farko a karamar hukumar da aka taba yi masa haka.
Taron lakcar ya sami halartar manyan karamar hukumar da suka hada da hakimai, tsoffin shugabannin karamar hukumar, ‘yan kungiyoyi da kuma sauran al’ummar karamar hukumar.