For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Shugabannin Da Suka Rantse Da Littafi Mai Tsarki Bai Kamata Su Wulakanta Aikinsu Ba – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga shugabanni wadanda suka rantse da littafi mai tsarki lokacin da suke karbar rantsuwa da kar su manta da amanar shugabancin da Allah da mutane suka dora musu.

Shugaban ya baiyana hakan ne a yayin da yake cewa ba ya da nufin tsayawa a mulki sama da wa’adi biyun da kundin tsarin mulki ya ware masa a matsayin Shugaban Najeriya.

Mai Baiwa Shugaba Buhari Shawara Kan Harkokin Yada Labarai, Femi Adesina, ya baiyana cewa, Shugaban ya baiyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara fadar Sarkin Lafia, Justice Sidi Bage Muhammad mai Ritaya a yau Alhamis yayin kaddamar da wasu aiyuka a jihar ta Nasarawa.

“Shi Sarki yana da dogon zango, A kundin tsarin mulki mu (zababbu) ba haka muke ba. Ba zan iya haura zango biyu ba kuma na rantse da Al-Qur’ani mai Tsarki cewar zan yi biyayya ga kundin tsarin mulkin Najeriya.

“Mu ajjiye maganar siyasa a gefe, duk lokacin da aka samu muka rantse da Al-Qur’ani, ya kamata mu kula sosai. Dole ne mu tabbatar ba mu bijirewa amanar da Allah ya dora mana ba a matsayinmu na shugabanni.

“Na ga tsofin gwamnoni a nan, kuma nima ina jiran lokacin da zan zama tsohon Shugaban Kasa,” in ji Buhari.

Femi Adesina ya ce, Buhari ya godewa mutanen Jihar Nasarawa game da tarbar da sukai masa inda ya baiyana jin dadinsa bisa canjin da Arewa ta Tsakiya ta samu tun zuwansa a shekarar 2019.

A bangarensa, Sarkin, wanda shine Shugaban Majalissar Sarakunan Jihar Nasarawa, ya fadawa Shugaban Kasa cewa, samar musu da tashar samar da wutar lantarki ta magance matsalolinsu kashi 80 cikin 100.

“Mutanenmu ba su taba jin dadi irin haka ba. Mutanenmu sun dawo rayuwarsu ta ainihi ta harkar sana’o’i,” in ji Sarkin.

(PUNCH)

Comments
Loading...