Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz dake ziyara a Rasha, sun jadadda bukatar kaucewa shiga yaki kan batun Ukraine, tare da warware rikicin ta hanyar diflomasiyya.
Yayin wani taron manema labarai tare da Mr. Scholz, shugaba Putin ya ce, su ma ba sa son shiga yaki, shi ya sa ma suka gabatar da shawarar yadda za a yi sulhu, a kokarin cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da tsaro ga kowa.
A nasa bangaren, Alof Scholz ya ce, nahiyar Turai na fuskantar rikici mafi hadari da ba a gani ba cikin gomman shekaru, kuma akwai bukatar yayyafawa batun na Ukraine ruwan sanyi, domin kaucewa aukuwar yaki.
Shugaba Putin ya kara da cewa, dage shigar Ukraine cikin kungiyar tsaro ta NATO ba zai amfanawa Rasha da komai ba, kuma Rashar na son a dauki batun tsaronta da muhimmanci.
Ya ce Rasha za ta dauki matakai bisa duk shirin da aka yi, kuma matakanta za su nuna ainihin yadda abubuwa ke gudana, amma babu wanda zai iya hasashen abubuwan da za su kasance, yana mai cewa, duk da haka, Moscow za ta yi kokarin warware batun ta hanyar diflomasiyya.
(RFI Hausa)