Matashi dan kishin kasa, masanin siyasa da mutumcin mutane, mai shaidar digiri a fannin siyasa, da gogewa a fannin mu’amala da al’umma, Ado Maje Saleh (Mai Ritaya), zai zama tsanin cigaban matasan Birnin Kudu a fannoni da dama idan ya samu dama.
A matsayin Dan Majalissar Jiha mai wakiltar Birnin Kudu a Majalissar Jihar Jigawa, Ado Maje ya shirya tsaf domin kawo gagarumin canji mai ma’ana a fannin tattalin arziki da zamantakewar matasa, mata da sauran al’ummar Karamar Hukumar Birnin Kudu.
A matsayinsa na Sojan Ruwa Mai Ritaya, wanda ya zagaya a fadin Najeriya da ma wasu guraren, Ado Maje ya gano hanyoyi da dama da zai bayar da gudummawa wajen bunkasa karamar hukumar Birnin Kudu ta yanda za ta kara yin fice a jerin kananan hukumomin Najeriya.
Matashi ne mai karancin shekaru da tarun ilimi da kuma sanin manya da girmamasu, idan har ya samu dama, Ado Maje zai samar da ingantaccen wakilci wanda zai bunkasa rayuwar kowa da kowa ba tare da nuna banbanci ba.
Abun da na fuskanta game da shi shine, Ado Maje ba ya neman takara saboda neman daukaka, sai dai yana neman takara ne domin ya yiwa al’ummarsa hidima.
A ko da yaushe Ado Maje burinsa shine a bar mutane su nuna damar da Allah ya ba su ta zabe, kuma su zabi cancanta, inda a ko yaushe yake nuna jajircewarsa wajen ganin ya yiwa al’ummarsa wakilci na gari.
Domin samun damar morar tanadin alherin da wannan bawan Allah, Ado Maje yai, ina kira ga duk kanin masu ruwa da tsaki a har zabe, kama daga kan masu zabe da kuma jam’iyyarmu ta APC da su baiwa hazikin matashin dama.
Haka kuma, ina kira ga Ado Maje da ya cigaba da jajircewa wajen tabbatar da kudirinsa na ciyar da al’ummarsa gaba, mu muna tare da shi domin mun amince da manufarsa ta alkhairi.
Ra’ayi: Wilfred Jibril