Daga: ZUNNURA ISAHAQ JIBRIEL
Ina ganin ya kamata matasan mu na yankin Arewacin Najeriya su fahimci Banbancin dake tsakanin SIYASA da kuma ADAWA, Domin a dogon nazarin da nayi na lura yawancin matasa basu iya bambanta tsakanin Adawa dakuma Siyasar kanta.
Abin da yasa na ware matasa shine: Matasane kaso mafi yawa a siyasar Duniya bama Najeriya ba, Kana Matasa ne ginshiƙin samun Nasara ko akasinta a kowace irin Tafiya ta siyasa, da sauran Dalilai. Don haka kenan yafi kyautuwa duk sanda zamuyi magana mufi maida Hankali kan Matasan.
– Da farko dai SIYASA na Nufin ayyukan da ke da alaƙa da mulkin ƙasa ko yanki, da kuma musayar ra’ayoyi tsakanin ɓangarorin da ke da iko dakuma waɗanda ake da iko akansu ta fuskar lamuran da suka shafi harkokin gwamnati, hukumar, da kuma sauran harkokin jama’a dana diflomasiyya.
Misali: Idan aka ce wannan dan Takara sanin matsalolin mutane, da yankunan mutanen dakuma nemo hanyoyin gyarawa ko yunkurin gyaran, saidai kash! A yanzu wadanda basu ma san menene matsalar mutane ba ko hanyoyin gyarawa na kururuwar kiran kansu da yan siyasa. Sannan wadanda basu san hanyoyin magance matsalolin A’umma bam ana wannan ikirari na kiran kansu yan siyasa, kana akwai wadan da sun san matsalar kuma sunsan hanyoyin gyaran matsalar amma basaso su suyi gwagwarmaya da hobbasa wajen bada gudunmawa akan gyara ko kawo sauyi, wadanda suma wadan nan rukuni na mutane suma ba za’a kirasu ‘yan siyasa ba.
A takaice dai ni ta bangarena ina ganin Siyasa itace sanin matsala da hanyoyin gyara domin sauyawa mutane hali, da kuma yanayin da suke ciki, kuma duk wanda bai cika wannan sharuda ba tofa ba cikakken dan siyasa bane.
-A wata gaɓar kuma SIYASA na ɗaukar ma’anar bibiyan ayyukan Gwamnati da nufin inganta yanki ko ƙasa, akwai kuma Tabbatar da matsayin wani ko ƙara masa ƙarfi irin na iko a ƙungiyan ce.
Ita kuwa ADAWA a siyasance shine kin wani abu da ake gudanarwa wanda ake tunanin akwai rashin daidai ko rashin dacewa, sakamakon sabanin ra’ayi ko Akida kokuwa manufofin siyasa.
Misali: gwamnati ta kawo wani tsari da take ganin za’a samu sauyi ko ci gaba, amma wata jam’iya ko kungiya ko wasu mutane suga akwai wata hanya datafi wannan tsarin da gwamnati takawo sauki ko sassauci, kokuma ma suga sam hakan bai kyautuba, kokuwa suce a’a ba wannan ce matsalar A’umma ba.
Zanso na buga misali da wani abu da yafaru a kasar Amurka lokacin da Shugaban kasar Barack Obama yake Mulki, a lokacin gwamnatinsa tazo da wani tsari na samar da lafiya mai suna OBAMA CARE, wani tsarine da ake saukakawa kowane ba’amurke a fannin lafiya. To saidai a wancan lokacin ‘yan jam’iyar REPUBLICAN masu adawa sun kalubalanci tsarin saboda suna ganin tsarin ya fadada ta yadda har wadanda ma ba ‘yan Asalin Amurka ba ma na morar tsarin.
Abin lura shine ita manufa kokuma banbancin manufa shine Adawa a siyasance, kuma ana Alkalancin kowane tsari ko manufar siyasa ne da karfin hujjoji da kuma manufa.
Abin Lurar shine, yanzu muna kan wani ƙadami da zaka kasa bambance shin matasan mu SIYASA suke ko ADAWA? Saboda idan sukace siyasar saikaga akwai gyara har wayau idan Adawar ma sukace saikaga abun ba daidai bane, a iyakacin binciken danayi nafi samun bayaninAbunda yawanci akeyi a yanzu yafi kama da wata kalma mai KIYAIYA ba ADAWA ko SIYASA ba. Saboda rashin manufa saikaga kowa yak ama gabansa, wasu sun tsani wasu, wasu basa Magana da wasu, wasu na yakar wasu, wasu na jin haushin wasu ba gyaira babu dalili.
Ina Mafita?
Cikin Ikon Rabbi Zanzo da Bayanin Mafita a Rubutuna na Gaba.
YARJARIDA,
ZUNNURA ISAHAQ JIBRIEL