Rahotanni sun nuna cewa, sojoji sun kubutar da mutane 8 da aka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna kamar yanda Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya sanar.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, ‘yan ta’adda uku sojojin suka kashe a hare-haren da suka kai kananan hukumomin Chikun, Igabi, da Giwa na jihar.
KU KARANTA: Sojoji Sun Yi Nasara Kan Boko Haram Da ISWAP Tare Da Kwace Bindigar Kakkabo Jirgi
Aruwan, wanda bai baiyana yanayi ko lokacin da aka kaddamar da hare-haren ba, ya sanarwa ‘yan jaridu hakan ne a yau Talata, inda ya ce jihar ta samu labarin ne daga sojoji.
Kwamishinan ya ce, “rundunar sojoji ta sanar da jihar Kaduna cewa, sojoji sun yi arangama da ‘yan ta’adda inda sukai nasara kan ‘yan ta’adda a kananan hukumomin Chinkun da Igabi.
Kwamishinan ya kuma rawaito Gwamna Nasir El-Rufa’i na nuna gamsuwarsa da kokarin sojojin.