Rukuni na Biyu na Sojojin Hadin Guiwa da ke Aiki a Arewa Maso Gabas, wato Operation Hadin Kai, sun yi nasara kan ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP wadanda sukai yunkurin kai hari garin Biu na jihar Borno.
Daraktan Hulda da Jama’a na Sojoji, Brigadier General Onyema Nwachukwu ne ya sanar da haka a yau Lahadi.
Nwachukwu ya ce, ‘yan ta’addar sun hadu da gamonsu ne lokacin sojojin bataliya ta 231 da kuma rundunar kakkabe makamai ta 331 sukai musu kwanton bauna a kauyen Maina Hari da ke yankin Biu a jiya Asabar.
KU KARANTA: Hukumar NDLEA Ta Kama Kwayoyi Miliyan 1.5 Na Tramadol A Hanyar Zuwa Kebbi
A cikin sanarwar ta sa, Nwachukwu ya ce, “a fadan da akai, sojoji sun nuna karfin kwarewarsu a kan ‘yan ta’addar inda suka sami nasarar kashe biyar daga cikinsu tare da tirsasawa sauran janyewa cikin nadama.
“Sojojin sun kuma kama motar harbi guda daya, bindigar kakkabo jirgi guda daya, babbar bindiga kirar HK 21 guda daya, babban bomb da ake sawa a makami mai linzami guda daya, harsasan kakkabo jirgi masu tsayin milimita 12.7 guda 137 da sauran abubuwa daga ‘yan ta’addar.
“Yanzu haka sojojin ba su kyalesu ba, suna bibiyarsu domin kawo karshensu,” in ji Daraktan.