For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sojojin Najeriya Da Na Birtaniya Za Su Yi Aiki Tare Wajen Kawo Ƙarshen Boko Haram – Badaru

Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar ya ce, Najeriya za ta ƙarfafa alaƙa da ƙasar Birtaniya domin magance matsalar tsaro a Najeriya.

Badaru ya bayyana hakan ne a yau, lokacin da wakilan ƙasar Birtaniya ƙarƙashin Ministan Sojojin Ƙasar, James Heappey su ka kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja.

Victoria Agba-Attah, Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’ikatar Tsaro ta fitar da sanarwa ga manema labarai.

Badaru ya bayyana cewar, Birntaniya na bayar da gudunmawa wajen tabbatar da tsaron hanyoyin ruwa na Najeriya, inda ya ƙara da cewar matsalar tsaro tana da faɗi da ƙalubale mai yawa.

KARANTA WANNAN: Ƴan-Ta’adda 41 Ne Suka Mutu A Faɗan Da Ya Ɓarke Tsakanin Boko Haram Da ISWAP A Borno

Ya ƙara da cewar, Sojojin Najeriya da na Birtaniya za su yi aiki tare wajen kawo ƙarshen hare-haren ƴan Boko Haram, inda ya ce akwai buƙatar Yammacin Duniya ya bayar da temako ga Najeriya kamar yanda ya ke bai wa sauran ƙasashe.

A nasa ɓangaren, Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya ce, da ma tun da jimawa Najeriya tana da kyakkywar alƙa da Birtaniya, inda ya ƙara da cewar, Najeriya ta ƙara ƙaimi wajen ganin ta kawo ƙarshen ta’addanci da ƴan-bindiga a ƙasar.

Tun farko a jawabinsa, Ministan Birtaniya, Heappey ya ce, sun kawo ziyarar ne domin su faɗaɗa gudunmawarsu ga sojojin Najeriya gwargwadon buƙatar da ake da ita ta tsaro.

NAN

Comments
Loading...