For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Sojojin Nijar Sun Naɗa Wani Masanin Tattalin Arziƙi A Matsayin Firaminista

Kusan mako biyu da sojoji suka karɓe mulkin Jamhuriyar Nijar, masu juyin mulkin sun bayyana sunan tsohon ministan tatattalin arziƙi, Ali Mahamman Lamine Zeine a matsayin sabon firaministan ƙasar.

A jiya da daddare ne, mai magana da yawun mulkin sojojin ya sanar da naɗin.

Shi dai sabon firaministan na Nijar, tsohon ministan tattalin arziƙi da kuɗaɗe ne na tsawon shekaru a gwamnatin Tandja Mammadou wanda aka kawar a shekarar 2010, sannan kuma a kwanan nan ya yi aiki da Bankin Ci Gaban Afirka a Ƙasar Chadi.

A ƙarshen watan Yuli ne dai, sojoji suka kawar da gwamnatin demokaraɗiyya ta Mohammed Bazoum sannan kuma suka ajjiye amfani da kundin tsarin mulkin ƙasar mai mutane sama da miliyan 26.

Wa’adin mako gudan da Ƙungiyar ECOWAS ta bai wa masu juyin mulkin na su dawo da Bazoum kan karagar mulki dai ya ƙare a ƙarshen makon da ya gabata.

Yanzu shugabannin ƙasashen Ƙungiyar ECOWAS zasu zauna domin ɗaukar mataki kan lamarin Nijar a ranar Alhamis mai zuwa a Abuja, biyo bayan ƙarewar wa’adin da suka bayar, wanda suka ce idan ba a cika ba, zasu ɗau matakin soji.

Comments
Loading...