Gwamnatin Sudan ta Kudu ta yi watsi da rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke zargin manyan masu mulkin kasar da wawashe miliyoyin daloli daga asusun gwamnatin kasar.
A makon da ya gabata ne dai Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu ta ce, an karkatar da makudan kudade da sauran nau’ikan dukiya daga aljihun gwamnati da yawansu ya zarce dala miliyan 73 tun daga shekarar 2018, tare da sace kusan dala miliyan 39 cikin kasa da wata biyu.
Hukumar ta yi gargadin cewa satar na iya lalata tsarin zaman lafiya da tuntuni ya kasance mai rauni a Sudan ta Kudun, kasar da har yanzu ke fafutukar murmurewa daga yakin basasar shekaru biyar da tayi fama da shi, bayan samun ‘yancin kai a shekarar 2011.
Sai dai ministan harkokin cikin gidan Sudan ta Kudu, Martin Elia Lomuro, ya yi watsi da rahoton, wanda ya bayyana a matsayin wata makarkashiyar hukumomin kasa da kasa ga zaman lafiyar kasar.
Lomuro ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa hukumomi ire-iren na kare hakkin dan adam da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya ba sa kaunar ci gaban Sudan ta Kudu, hakan ya sa suke kirkirar rahotannin karya a fannoni daban daban, musamman kan abin da ya shafi rashawa da kuma hakkin dan Adam.