Daga: Abdurrahman Zubairu
Me Ake Nufi Da IJMB?
Haruffan IJMB na nufin Interim Joint Matriculation Board, matakin karatu ne na gaba da Sakandare wanda Ma’aikatar Ilimi ta Kasa ta sahhalewa Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya ta dinga gudanar da shi; hadin guiwa da wasu daga cikin makarantun gaba da Sakandare na fadin Kasar ta hanyar affiliation da kuma sauran cibiyoyi da aka bubbude domin gudanar da tsarin.
An kirkiri wannan tsari ne domin bada horo ga Daliban da suka kammala karatun Sakandare suke kokarin neman gurbin karatu a Jami’a, ya zama share fage kenan na shiga Jami’a.
Abin da ake bukata daga mai neman shiga wannan tsari shi ne kwalin Sakandare, hakazalika wanda ya kammala karatun amma sakamakonsa bai zo hannu ba wato yana jira zai iya neman shiga tsarin.
IJMB tsari ne da Gwamnati ta sahhale a nemi gurbin karatu a Jami’a da shi, walau Jami’o’in Kasarmu Najeriya ko na ketare.
A kowacce shekara akalla Dalibai Dubu Ashirin (20,000) ne ke shiga cikin tsarin, yayin da kashi Saba’in da Biyar daga cikinsu ke samun guraben karatu a Jami’o’i daban-daban da kuma fannoni daban-daban da suka zaba.
An sahhale cewa duk Dalibin da yayi wannan tsari a bashi gurbin karatu a mataki na biyu (Level 200) kwatankwacin masu kwalin Diploma da NCE babu wata bambantawa.
Masu sha’awar shiga wannan tsari zasu zabi darussa Uku (3) (Three Subjects) masu alaka da fannin da suke da burin karantawa a Jami’a, za a shafe tsawon shekara daya (1) ana koyar da su wadannan darussa, daga karshe za ayi musu jarrabawa, wadanda jarrabawarsu ta cika sharudda zasu nemi guraben karatu a Jami’o’i da takardar shaidar kammalawa da aka basu (Certificate) ta hanyar (Direct Entry).
Wannan tsari yana gudana ne cikin shekara daya, ana fara shi daga watan Uku (March) a kuma kammala shi a watan daya (January) yayin da ake yin jarrabawar kammalawa a watan biyu (February), jimillar watanni sha biyu (12) kenan.
IJMB yana da fannoni uku na karatu (Arts, Sciences da Social and Management Science).
IJMB a Sule Lamido University
Kamar sauran manyan makarantun gaba da Sakandare ita ma Jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa a jihar Jigawa tana gudanar da wannan tsarin karatu.
A yanzu haka shafin rijista domin shiga wannan tsari a wannan makaranta yana bude ga masu neman shiga tun daga ranar Litinin 10/01/2022 zuwa 30/01/2022.
Sharuddan da ake bukata daga mai neman shiga su ne akalla Credit biyar a Jarrabawar Sakandare hade da darasin Turanci ga ‘yan fannin Art da kuma darasin Lissafi ga ‘yan fannin Science, sannan hade da daya daga cikinsu ga ‘yan fannin Social and Management Science.
Domin neman shiga wannan tsari a ziyarci shafin yanar gizo da makarantar ta ware domin haka: admissions.slu.edu.ng/ijmb, a shigar da duk bayanan da aka bukata gwargwadon abin da ake nema.
Bayan wannan kuma akwai rana da wannan makaranta ta ware domin tantance masu neman, za ayi wannan tantancewa kamar haka: Ranar Talata da Laraba (08/02/2022 – 09/02/2022) a cikin makarantar dake kan titin Kano zuwa Jahun, Kafin Hausa, jihar Jigawa da misalin karfe 09:00 na safe.
Darussan da wannan makaranta take gudanarwa sun hada da:
Fannin Science
- Biology/Chemistry/Physics
- Biology/Chemistry/Mathematics
- Biology/Chemistry/Geography
- Chemistry/Geography/Mathematics
- Chemistry/Geography/Physics
- Chemistry/Physics/Mathematics
Fannin Arts
- Arabic/Government/Hausa
- Arabic/Government/Islamic Studies
- Arabic/Hausa/Islamic Studies
- Arabic/Hausa/Literature
- Arabic/History/Islamic Studies
- Hausa/Arabic/History
- Hausa/Islamic Studies/History
- History/Islamic Studies/Literature
- Government/Islamic Studies/Hausa
- Government/Islamic Studies/Literature
Fannin Social and Management Sciences
- Accounting/Business Management/Mathematics
- Accounting/Business Management/Economics
- Accounting/Business Management/Geography
- Accounting/Business Management/Government
- Accounting/Business Management/Sociology
- Accounting/Economics/Geography
- Accounting/Economics/Mathematics
- Accounting/Economics/Government
- Accounting/Economics/Sociology
- Accounting/Geography/Mathematics
- Accounting/Geography/Government
- Accounting/Geography/Sociology
- Accounting/Government/Mathematics
- Accounting/Government/Sociology
- Economics/Geography/Mathematics
- Economics/Government/Sociology
- Economics/Geography/Government
- Economics/Geography/Sociology
- Geography/Government/Sociology
- Business Management/Economics/Geography
- Business Management/Economics/Government
- Business Management/Economics/Mathematics
- Business Management/Economics/Sociology
Abdurrahman Zubairu
Raudha Media Services, Birnin Kudu
raudhabkd.ng@gmail.com, 09064114593