Jam’iyyar PDP ta gargaɗi gwamnatin jam’iyyar APC a kan matsin da take zargin ta saka ƴan Najeriya wanda hakan kan iya saka ƴan kasar fitowa kan titi domin gudanar da zanga-zanga.
PDPn ta ce, ‘yan Najeriya za su iya yin bore a kan zalunci, cin hanci da rashawa, rashin damuwa da halin da al’umma suke ciki kan halin da aka shiga sanadiyyar shigowa da gurɓataccen man fetir cikin ƙasar.
PDPn ta baiyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Debo Ologunagba ya sanyawa hannu kuma a rabawa manema labarai a yau Laraba.
PDPn ta ce, “Jam’iyyarmu ta yi allawadai da yunƙurin da gwamnatin APC take na sake ɗaukar kuɗaɗe har sama da naira biliyan 201 domin samar da wani man da zai maye gurbin wannan gubataccen maimakon a damko waɗanda suka aikata wannan aika+aikar don su fuskanci hukunci.
“Babu abun mamaki idan APC ta yi watsi da kiran da ƴan Najeriya suke mata na samar da sauƙi da kuma kawo ƙarshen cin hanci da matsin da wannan gwamnatin ta kawo saboda tsabar rashin ƙwarewarsu.”
Sanarwar ta kara da cewa, “A bayyane take wannnan wani salo ne da gwamnatin APC take ƙoƙarin sake wawure kuɗaɗen ƙasar nan domin yin amfani da su wajen tafka maguɗi a zaɓen 2023 da kuma jin daɗin rayuwar jagororinsu su yayin da su kuma ƴan Najeriya ko oho.
“Irin wannann muguwar satar da rashin imanin APC kan iya kai ƴan Najeriya bango. Babu wani wanda APC za ta zarga idan ƴan Najeriya suka yi mata bore saboda nuna halin ko in kula, rashin imani da rashin ƙauna da take nunawa ƴan Najeriya.
“Ya kamata kowa ya sani har yanzu APC ba su ce komai akan kiran da muka yi musu na su gudanar da bincike akan zargin da ake na wasu daga cikin jagororin APC sun haɗa kai da wasu ƴan ƙasashen waje don shigowa da man fetur mai araha domin samun biliyoyin nairori da za su yi amfani da su wajen tafka maguɗi a babban zaɓen 2023.
“Ƴan Najeriya sun san yadda jam’iyyarmu da sauran ƴan Najeriya masu kishi muka yi ta faɗi tashi don ganin APC ba su samu damar wawure naira tirilyan 2.557 a matsayin tallafin man fetur ba. Tun da asirinsu ya tonu a nan, shi ne APC suka huce akan ƴan Najeriya ta hanyar shigo da gurɓataccen man fetur domin su ce za su kashe biliyan 201 don wanke gurɓataccen man,” in ji sanarwar.