For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

TALLAFIN MAI: Ku Shiryawa Zanga-Zanga – Kungiyar Kwadago Ga Kungiyoyi

Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC ta umarci mambobinta, bangarorinta, da kungiyoyin cigaban al’umma da ke da alaka da kungiyar, da su shiryawa zanga-zanga wadda aka shirya yi a duk fadin Najeriya ranar 27 ga watan Janairu da kuma 1 ga watan Fabarairu domin kalubalantar shirin Gwamnatin Tarayya na cire tallafin mai.

Kungiyar NLC ta kuma bukaci bangarorinta a duk fadin kasa, da su shirya mambobinsu domin zanga-zangar tare da tabbatar da an yi biyayya ga tsarin zanga-zangar na kasa.

Wannan shine abun da aka yanke a zaman tattaunawar da Kungiyar NLC ta yi tare da shugabannin kungiyoyin al’umma wanda Shugaban Kungiyar, Ayuba Wabba ya jagoranta a Gidan Ma’aikata da ke Abuja a ranar Talata.

KU KARANTA: An Yi Kira Ga Buhari Da Ya Dawo Da Farashin Gas Yanda Ya Sameshi A 2015

Wani mamba a Kwamitin Gudanarwa na NLC wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce, shugabanni da sakatarorin bangarorin NLC sun yi alkawarin shirya mutanensu domin zanga-zangar.

Ya bayyana cewa, “An bukaci da mu je mu shirya mambobinmu a duk fadin kasa saboda zanga-zangar da aka shirya gudanarwa ranar 27 ga watan Janairu.

“Kowanne bangare an bukaci da ya shirya mambobi masu yawan da zai iya saboda zanga-zangar ta yi inganci sosai. Gagarumin gangami shine abin da muke bukata ga zanga-zangar da aka shirya.

“Kowanne shugaba da babban sakatare na bangare sun yi alkawarin bayar da goyon baya ga wannan zanga-zanga.

“Kungiyoyin al’umma na aiki tare da Kungiyar Kwadago. Kungiyoyin al’ummar da muke aiki tare da su za su kasance tare da mu a zanga-zangar ranar 27 ga watan Janairu.”

Ya kuma tabbatar da cewa, Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ba za ta bari shirin cire tallafin mai ya kai ga nasara ba, inda ya kara da cewa, “idan har aka cire to zai zama bala’i ga dukkaninmu a kasar.”

Idan za a tuna, Gwamnatin Tarayya, a shekarar da ta gabata ta sanar da cewa ta shirya cire tallafin mai a farkon wannan shekara da muke ciki.

Comments
Loading...