Bude asusun banki domin karbar tallafin naira 5,000 ga mata masu ciki a jihar Jigawa ya jawo tsaiko ga fara shirin bayar da tallafin.
Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya baiyana haka lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan tsaikon da aka samu a shirin baiwa matan tallafin.
Umar Namadi ya ce, gwamnatin jihar ta sanya shirin a kasafin kudin 2021 da 2022, to amma bude asusun banki ga masu morar tallafin ya gamu da matsala.
Umar Namadi ya baiyana cewa, gwamnatin jihar ce ta kirkiro da shirin domin zaburar da matan karkara kan zuwa awo da kuma haihuwa a asibiti.
Ya kara da cewa, tallafin kudin na wata wata zai kuma temakawa matan wajen siyan abincin da zai kara musu lafiya da kara lafiya ga jariran da suke dauke da su domin gujewa fadawa matsalolin yunwa.
Mataimakin Gwamnan ya kuma ce, cikin mata 5000 da za su mori shirin, gwamnatin ta samu nasarar budewa mata 3,800 asusun, sannan kuma ta yanke hukuncin fara biyan tallafin a wannan watan.