For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tallafin Naira Biliyan Biyar Ba Zai Magance Talauci Ba, In Ji NLC

Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya, NLC, Joe Ajero ya bayyana cewar, tallafin naira biliyan biyar ga kowacce jiha, wanda Gwamnatin Tarayya ta sanar bai kai kowa ya samu naira dubu 1500 ba, idan aka raba wa ƴan Najeriya sama miliyan 133 da ke cikin ƙangin talauci.

Ajero wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’a a tattaunawarsa da gidan talabijin na CHANNELS a shirin POLITICS TODAY, ya ce babu yanda za a yi naira biliyan 185 ta yi wani tasiri idan aka raba ta ga ƴan Najeriya miliyan 133 da ke cikin ƙangin talauci, kamar yanda ƙidddigar Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta nuna.

KARANTA WANNAN: Gwamnoni Ba Abun Yarda Ba Ne Kan Tallafin Da Za A Rabawa Talakawa – NLC

Ya ce, idan za a mayar da kuɗin zuwa tsabar shinkafa, bai fi kowa ya samu kofi ɗai-ɗai ba, idan aka raba.

Ya ƙara da cewar, daga lokacin da aka ƙara kuɗin man fetur a karo na farko zuwa ƙarin da aka yi na ƙarshe, ƴan Najeriya da dama sun shiga cikin matsanancin talauci.

Comments
Loading...