For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

TANTANCE MINISTOCI: El-Rufa’i Ya Fuskanci Ƙalubale Daga Sanatan Kogi

Ɗan Majalissar Dattawa da ke wakiltar Mazaɓar Sanata ta Kogi ta Yamma, Sanata Sunday Karimi ya ƙalubalanci tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i a lokacin da sanatoci ke tantance a shi a yau Talata.

Bayan El-Rufa’i ya kammala gabatar da kansa a gaban sanatocin ne dai, Karimi ya shaidawa cewa akwai ƙorafi da aka rubuto a kan tsohon gwamnan kan matsalar tsaro da ke faruwa a yankin Kudancin Kaduna.

Karimi ya nunawa Shugaban Majalissar Dattawa embulam yana mai bayyana cewa, yana da ƙorafin da aka rubuto kan tsaohon gwamnan kan matsalar tsaron da ta faru a yankin Kudancin Kaduna lokacin yana matsayin gwamna a jihar, ya nemi a ba shi dama ya karanta ƙorafin.

Da farko dai, El-Rufa’i ya bayyanawa sanatocin irin nasarorin da ya samu a matsayinsa na gwamna da kuma ministan Abuja, kafin daga bisani a baiwa sanatocin damar yi masa tambayoyi.

To sai dai kuma bayan amsa tambayoyin da Sanata Abdulaziz Yari yai wa masa, Shugaban Majalissar Dattawa, Godswill Akpabio ya umarci El-Rufa’i da yai gaisuwa ga sanatocin ya wuce bayan Sanata Suleiman Kwari ya buƙaci hakan ga majalissar.

Sanata Akpabio, wanda ya ƙi yarda da buƙatar Sanata Karimi ya bayyana cewa, akwai ƙorafe-ƙorafe da dama da aka gabatar a kan da dama daga waɗanda ake son naɗawa ministocin.

Ya bayyana cewa, zauren majalissar ba wajen karɓar ƙorafe-ƙorafe ba ne, sanatocin zasu zauna kan ƙorafe-ƙorafen tare da miƙa su ga hukumomin da suka kamata.

Comments
Loading...