For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tattalin Arzikin Najeriya Ya Karu Da Kashi 3.98% A Watanni Ukun Karshen 2021

Tattalin arzikin GDPn Najeriya ya karu da kashi 3.98 bisa 100 sakamakon sauye sauyen da aka samu tsarin tattalin arzikin kasar a rubu’i na hudu na shekarar 2021, inda ya samu farfadowa daga mawuyacin yanayi.

A rahoton baya bayan nan da hukumar kididdigar kasar NBS, ta fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa, rubu’i na hudu ya nuna yadda tattalin arzikin kasar ke farfadowa wanda karuwarsa ta kai kashi 3.40 bisa 100 a shekara.

Sanarwar ta ce, karuwar da aka samu a rubu’i na hudun ya dara karin kashi 0.11 bisa 100 da aka samu a rubu’in farko na shekarar da ta gabata, kana kasa da kashi 4.03 da aka samu a rubu’i na uku na shekarar 2021.

A bisa matakin rubu’i zuwa rubu’i, hakikanin karuwar GDPn kasar ya kai kashi 9.63 bisa 100 a rubu’i na hudu idan an kwatanta da rubu’i na uku, wanda yake nuna an samu matukar karuwar harkokin tattalin arzikin kasar.

Karuwar GDPn da aka samu a rubu’i na hudu na shekarar 2021 ya zarce wanda aka samu idan an kwatanta da kashi 10.07 bisa 100 da aka samu a rubu’i na hudu na shekarar 2020, sai dai ya yi kasa da kashi 15.41 bisa 100 na karuwar da aka samu a ragowar rubu’in da suka biyo baya.

Hukumar NBS ta kara da cewa, jimillar karuwar tattalin arzikin kasar da aka samu a shekarar 2021 ya kai kashi 13.92 bisa 100.

(CRI Hausa)

Comments
Loading...