Ana hasashen tattalin arzikin Najeriya zai karu da kaso 2.5 cikin 100 a shekarar 2022 da muke ciki in ji Bankin Duniya.
Bankin, a rahotonsa na Janairun 2022 kan Cigaban Tattalin Arzikin Duniya wanda aka wallafa ranar Talata, an yi hasashe cewa, tattalin arzikin Najeriya zai karu kaso 2.5 cikin 100 a shekarar 2022 da kuma kaso 2.8 cikin 100 a shekarar 2023.
An alakanta cigaban da za a samu da hauhawar farashin mai da kuma cigaban fasahar zamani da hada-hadar kudade.
“Bangaren mai zai mori hauhawar farashi, da samun sassauci daga iyakancewar Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur, OPEC, da kuma gyaran tsare-tsaren gudanarwa,” in Bankin.
KU KARANTA: Ina Sane Da Irin Wahalar Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki – Buhari
“Aiyuka bangarorin gudanar da aiyuka ana tsammanin zai sa mu karuwa, musamman bangaren sadarwar zamani da kuma hada-hadar kudade.”
Haka kuma, dawowar annobar Korona ta jawo samun kudaden shiga da kuma raguwar aiyukan yi zai ragu a hankali, wannan tare da hawan farashin abinci, wadannan za su jawo tarnaki ga warakar da ake son samu a biyan bukatun mutane.
“Sabbin farmakin sabuwar samfurin Korona da karuwar hauhawar farashin kayayyaki, bashi, da karuwar rashin dai-daito a samun kudade zai jefa warakar da za a samu a kasashe masu tasowa,” in ji rahoton.
Rahoton ya kuma yi bayanin cewa, al’amura a bangaren da ba na mai ba zai tsaya saboda rikice-rikice da rashin zaman lafiya a wasu sassa na kasar hadi da sabuwar barazanar Korona.
Babban Bankin ya kuma yi hasashen cewa samun kudaden dai-daiku zai ragu a shekarar 2022 sama da yanda ya kasance shekaru 10 da suka gabata a kasashen Angola, Najeriya da kuma South Afrika.