For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tinubu Bai Yi Min Adalci Ba Da Ya Hadu Da Kwankwaso A Paris – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya nuna rashin jin dadinsa kan ganawar da tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso ya yi da Shugaban Kasa mai Jiran Gado, Bola Tinubu.

Gwamnan ya yi korafin ne a cikin wani faifan murya, wanda wasu suka tantance a matsayin muryoyin Ganduje da na tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC, Ibrahim Masari.

Ganduje dai ya taba fadawa cikin irin wannan fallasa a shekarar 2018, a wancan lokacin an ga Ganduje a cikin wasu faifan bidiyo da aka fallasa yana cusa daloli a cikin rigarsa, wanda ake kyautata zaton cin hanci ne da ake zargin ya karba daga hannun wasu ‘yan kwangila.

Tinubu a kwanan nan, ya gana da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP, a zaben 2023 a matsayin wani bangare na shirin kafa gwamnatin hadin kan kasa.

An gano cewa zababben shugaban a yayin ganawar ya mika wa Kwankwaso hannu tare da nuna sha’awar sa na yin aiki da shi.

Duk da cewa majiyoyi sun ce shugabannin za su yi taruka na gaba don kammala yarjejeniyar, amma an tattaro cewa shugaba mai jiran gado ya baiwa Kwankwaso mukamin minista.

Amma a cikin faifan sautin, an ji Ganduje yana kuka ga Masari cewa Tinubu bai yi masa adalci ba kan gayyatar Kwankwaso zuwa ganawa a birnin Paris.

A cikin faifan sautin, an ji Masari yana kwantar da hankalin Gwamna Ganduje tare da rokonsa da kada ya yi fushi kan abin da ya faru.

Ku danna kasa ku saurari faifan muryar:

MURYAR GANDUJE DA IBRAHIM MASARI KAN GANAWAR TINUBU DA KWANKWASO

Comments
Loading...