For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tinubu Na Ƙoƙarin Ɗabbaƙa Cigaban Ababen More Rayuwa Irin Na China A Najeriya

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna kudirinsa na kwaikwayon cigaban kasar Sin a fannin ababen more rayuwa a Najeriya bayan ziyararsa zuwa kasar.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawa da kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasar Sin (NIDO China) da al’ummar Najeriya da ke Beijing.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya ce tattaunawarsa da Shugaban kasar Sin Xi Jinping da halartarsa taron koli na Forum on China-Africa Cooperation (FOCAC) na shekarar 2024 ya nuna muhimmancin zuba jari a fannin ababen more rayuwa, cinikayya, hada-hadar kudi, makamashi, tattalin arzikin noma, da hakar ma’adinai.

Shugaba Tinubu ya jaddada bukatar samar da hanyoyin koyarwa na zamani da kuma ingantaccen yanayin kasuwanci mai habaka.

Ya yi kira ga ƴan Najeriya mazauna kasar Sin da su zama jakadun Najeriya nagari tare da wakiltar kasar cikin kima.

Ya jaddada muhimmancin ladabi da jajircewa wajen bautawa kasa, inda ya ba da misalin yanda kasar Sin take da al’umma mai ladabi da biyayya.

Shugaban kasa Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya mazauna kasashen waje cewa Bankin Masana’antu yana shirye ya hada hannu da su domin cin moriyar damarmaki a Najeriya.

Comments
Loading...