Akwai yiyuwar cewa, ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu zai baiyana wanda zai mara masa baya a matsayin ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa a ranar Laraba mai zuwa.
Ana sa ran Tinubu zai kammala tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyya da suka haɗa da gwamnoni a gobe Talata, sannan ya sanar da mataimakinsa a jibi Laraba.
Haka kuma, an gano cewar, gwamnonin APC da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, sun amince da cewa, mai marawa Tinubun a takarar ya fito daga yankin Arewa maso Gabas.
Yankin Arewa maso Gabas dai yana da jihohi 6 da suka haɗa da Borno, Yobe, Taraba, Adamawa, Gombe da kuma Bauchi.
A daidai lokacin da jam’iyyar ta amince da fitar da ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa daga Arewa maso Gabas, haka kuma, ta amince da idan ta ci zaɓe, Shugaban Majalissar Dattawa ya fito daga Kudu maso Gabas, sannan Arewa maso Yamma ta fitar da Kakakin Majalissar Wakilai.
Wani na kusa da Tinubu kuma Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Lagos yankin Tsakiya, Hakeem Bamgbala, a tattaunawarsa da PUNCH ya tabbatar da cewa Tinubu zai baiyana sunan ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa cikin kwanaki biyu zuwa uku masu zuwa.
Bamigbala ya kuma ce, jam’iyyar ba ta yanke hukuncin cewa, Tinubu ya zaɓo Musulmi a matsayin wanda zai mara masa baya ba, kamar yanda wasu ke ta raɗe-raɗi.
Ya ce, maganar ɗan takara Musulmi mataimaki Musulmi jita-jita ce kawai, inda ya ƙara da cewa, komai zai warware nan da kwana biyu zuwa uku, lokacin da jam’iyya zata sanar da sunan wanda zai marawa Tinubun baya.
Ya kuma yi kukan cewa, bai kamata wani ya fito ya ce, APC na ƙoƙarin tsayar da ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa Musulmi ba, inda ya ce, suna duba ingantaccen ɗan Arewa wanda yake Kirista domin marawa Tinubun baya a takarar Shugaban Ƙasa.
Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sanar da cewa, ranar Juma’a 17 ga watan Yunin da muke ciki ce ranar ƙarshe da kowacce jam’iyya zata miƙa sunayen ƴan takarar Shugaban Ƙasa da Mataimakansu.