Daga: Haruna Ahmad Bultuwa
Jagoran Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya bayar da hakuri game da kalamansa da yai da suka shafi Katin Zabe na Dindindin.
Idan za a tuna, a lokacin da Tinubu yake yiwa magoya bayansa jawabi a Abuja game da zaben 2023, ya yi kiransu da su je su sake rijistar zabe saboda katinsu ya gama aiki.
Ya ce, “Duk da ba su sanar da ku a kan lokaci ba, Katin Zaben da kuke da shi ya gama aiki. Ku tafi da dan gidanku daya, ‘yan gidanku biyu, ku kwankwasawa kowa, ku tabbatar cewa an yi sabuwar rijista . . . Saboda ta yiwu ba za su sanar da ku a kan lokaci ba, amma Katin Zaben da kuke da shi ya gama aiki. Tabbas!
“Akwai bukatar ku yada wannan a duk kananan hukumomi da mazabu a kowanne mataki. Komai wuyar hakan kuwa. A wajena ina ganin abun nan kusa ne, kuma ku kalli sauran zabubbuka da aka yi, za ku ga cewa suna samun koma baya, saboda katinan sun gama aiki. Dole ne ku je ku yi rijista domin ku yi zabe ku cimma burikanku. Allah ya temakeku ya temaki Nigeria.”
KU KARANTA: Zan Biyawa Kowanne Yaro WAEC In Na Zama Shugaban Kasa – Tinubu
Wannan jawabi na Tinubu ya sami martani daga Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta, INEC, inda ta bayyana kalaman a matsayin kuskure.
Hukumar INEC ta ce Katin Zabe na Dindindin ba sa zuwa da kwanan watan gama aiki.
A mayar da martanin da ya biyo bayan jawabin INEC kan kalaman Tinubu, sashin yada labarai na Tinubu ya bayyana a wata sanarwa cewa, kalaman jagoran APC sun zo ne a kuskure, inda yai amfani da ‘gama aiki’ maimakon sabuntawa.
Sanarwar ta ce, “A ranar Talata da daddare a Abuja, Asiwaju Bola Tinubu ya gana da wakilan mata daga Lagos da sauran sassan kasa, wadanda ke halartar Taron Mata na Jam’iyyar APC. A lokacin da yake baiwa matan shawara kan su duba yanayin katinan zabensu sannan su kira magoya baya wajen fita su yi zabe, ya kuskure wajen amfani da kalmar ‘expire’ maimakon ya ce zai yiwu akwai bukatar sabunta katinan.
“Hakan tana faruwa, ana sanar da shi, Asiwaju ya bayar da hakuri game da kuskuren cikin kalamansa, ya kuma yi nadamar matsalar da za su iya jawowa. Asiwaju Tinubu ya kuma bayyana jin dadinsa da kishin Hukumar INEC da ma’aikatanta wajen tabbatar da hanyoyin samun zabe mai inganci ga ‘yan Nigeria daga kowacce jam’iyya.”