Daya daga cikin na gaba-gaba a neman jam’iyyar APC ta tsayar da su takarar Shugaban Kasa a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu ya ce, shi ya jagoranci gwagwarmayar siyasar da ta kawo Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015.
Haka kuma, Tinubu ya baiyana karara cewa, shine ya bayar da sunan Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa ga Buhari.
Tinubu ya yi wadannan bayanai ne a Abeokuta, lokacin da yake jawabi ga taron deleget na jam’iyyar APC a daidai lokacin da ake shirin fara aiwatar da zaben fitar da gwani na Shugaban Kasa a jam’iyyar.
A lokacin taron, Tinubu yana tare da Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, takwaransa na Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da kuma tsohon Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima.
Tsohon Gwamna Tinubu, ya ce, ya yi wannan bayani ne a karo na farko a Jihar Ogun, jihar Osinbajo, daya daga cikin masu kalubalantarsa a neman tikitin jam’iyyar APC na takarar Shugaban Kasa.
Ya ce, Buhari ya ba shi damar tsayawa takarar Mataimakin Shugaban Kasa, amma wasu ‘yan gaza-gani suka kalubalanci hakan, suna tsoron abun da zai biyo bayan tikitin Musulmi da Musulmi.
Tsohon Gwamnan dai ya ce, lokacin da aka nemi da ya kawo sunayen mutane uku domin daya a cikinsu ya zama dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa, ya zana sunayen Yemi Kadoso, Wale Edun da kuma Yemi Osinbajo.
Ya kara da cewa, a karshe dai ya yanke hukuncin sanya Osinbajo a matsayin dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa.
“Ba ku taba jin haka daga gare ni ba a baya. Nan ne waje na farko da nake fadin hakan,” Tinubu ya fada ga delegets da yaren Yarabanci.
Da yake magana kan fitowar Buhari a wancan lokacin, Tinubu ya ce, “Ba don ni da na jagoranci yakin fafutukar ba, Da Buhari bai fito ba. Ya yi takara a karo na farko, na biyu da na uku amma duk ya fadi. Sai da ma ya fada a Talabijin cewa shi ba zai ma kara tsayawa takara ba.
“Amma ni na tashi na je gidansa a Katsina. Na ce masa zaka tsaya takara kuma zaka ci zabe, amma ba zakai wasa da al’amuran Yarabawa ba. Kuma tun da ya ci, ba ai min minista ba. Kuma ba a taba ba ni kwangila ba.
“Wannan karon, lokacin Yarabawa ne kuma kasar Yarabawa lokaci na ne.”
Tinubu kuma ya ce, ba don Allah ya ga dama ba, kuma shi Tinubun ya temaka ba, da Gwamna Dapo Abiodun bai ci zabe ba a zaben shekarar 2019.
“Dapo da ke zaune a kasa can, zai iya zama gwamna ba tare da ni ba? Muna filin wasa inda suka yayyaga duk fastocinsa. Har ita kan ta tutar jam’iyyar ba sa so su mika masa, nine nan wanda ya karbo ta.
“Idan yana son haduwa da Allah a yanayin da ya kamata, dole ne ya san cewa, ba don Allah da ni ba, da bai zama gwamna ba.”
A lokacin jawabinsa, Gwamna Dapo Abiodun wanda tun a farko ya nuna goyon bayansa ga takarar Osinbajo, ya ki yarda ya aminta da takarar Tinubu.
Ya fadawa Tinubu cewa, delegets daga jihar ta Ogun zasu yi “abin da ya dace” a wajen zaben fitar da gwanin.
Abiodun ya baiyana Tinubu a matsayin jarumin siyasa, mai yawan samun nasara da kuma iya tsare-tsare.