For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tinubu Ya Sa Jami’an Tsaro Su Ƙwato Bashin Da Aka Bai Wa Manoma Kafin Nan Da 18 Ga Satumba

Tsarin bayar da bashin noma na Anchor Borrowers da Babban Bankin Najeriya ya samar domin bunƙasa samar da amfanin gona a Najeriya ya shiga cikin garari saboda gazawar waɗanda suka mori shirin wajen biyan bashin da suka karɓa.

Rashin biyan na su kuma ya sanya gwamnati kasa ƙara bai wa wasu domin su ma su mori tallafin.

Jaridar VANGUARD ta gano cewar, cikin naira tiriliyan 1.1 da CBN ya rabawa manoma daga fara shirin na Anchor Borrowers iya naira biliyan 546 ne kaɗai ya dawo wajen bankin, yayin da naira biliyan 577 har yanzu yake hannun wasu manoman da su ka ƙi biya.

KARANTA WANNAN: Yawan Dogaro Da Bashi Ya Zo Ƙarshe A Najeriya – Tinubu

Wannan yawan kuɗi da ke hannun manoman ya dugunzuma Shugaban Ƙasa matuƙa, musamman ma da aka bayyana masa cewar, shirin zai iya samun tsaiko matuƙar ba a dawo da kuɗaɗen ba.

Wata runduna daga rundunonin jami’an tsaro na ƙasa, ta shaida wa VANGUARD cewar Shugaban Ƙasa, Tinubu, ya kira manyan jami’an tsaro na ƙasa inda ya ba su umarnin cewar su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun karɓo kuɗaɗen daga waɗanda suka ƙi biyan kafin nan da ranar 18 ga watan Satumba, 2023.

Shugaban Ƙasar ya ce, za a karɓo kuɗaɗen domin manoma na gaskiya waɗanda ke son bashin don bunƙasa harkar samar da abinci a ƙasa.

Comments
Loading...