Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa bisa yawan ma’aikatan da ke karɓar albashi a matakin ƙasa da sauran matakai.
Shugaban Ƙasar ya bayyana abin da ke zuciyarsa ne a jiya Litinin lokacin da ya ke magana a wajen wani zaman tattaunawa da Mataimakin Shugaban kamfanin Oracle na duniya, Mr. Andres Garcia Arroyo a fadarsa da ke Abuja
Tinubu ya faɗawa baƙon nasa cewar, da ci gaban da ake samu na fasahar zamani, Najeriya za ta mayar da aikin gwamnati kan tsarin na’ura mai ƙwaƙwalwa tare da sanya kuɗaɗen gwamnati wajen samun ci gaban tattalin arziƙi.
KARANTA WANNAN: Gwamnan Kano Ya Naɗa Ƙarin Masu Ba Shi Sahawara Guda 14 Da Masu Ba Shi Rahoto Guda 44
Ya ce, duk lokacin da aka miƙa masa yawan ma’aikatan da ke karɓar albashi yana shiga cikin firgici, inda ya ce ko ta yaya za a samu kuɗaɗen da za a gina ababen more rayuwar da ake buƙata idan har kaso 1 zuwa 2 cikin 100 na al’umma na cinye duk kuɗaɗen shigar da ake samu?
Tinubu ya ce, zai yi aiki da kamfanin Oracle wajen samar da daidaito da kuma lura da dukkan hada-hadar kuɗaɗen gwamnati, inda ya ƙara da cewar, yana da yaƙinin kamfanin Oracle zai iya aikin.
Shugaban Ƙasa Tinubu ya nuna goyon bayansa wajen yin haɗin guiwa da kamfanonin fasahar zamani domin tabbatar da cewar bayanan ma’aikatun gwamnati suna kan daidai da gaskiya.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Oracle na Duniya ya gabatar da tsare-tsaren yanda kamfaninsu zai sauya fasalin aikin gwamnati a matakin gwamnatin tarayya zuwa bin tsarin na’aura mai ƙwaƙwalwa domin a samar da bunƙasar tattalin arziƙi da samarwa gwamnati kuɗaɗe da kuma samar da ƙwarewa ga ƴan Najeriya.