Shugaban Kasar Najeriya mai Jiran Gado, Bola Ahmed Tinubu ya yi alwashin biyan ma’aikata albashin da zai ba su damar yin rayuwa ta mutunci da biyan bukatun iyalansu.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a matsayin murnan Ranar ma’aikata ta duniya, Tinubu ya bayyana cewa zai hada hannu da ma’aikatan kasar domin a yakar talauci da rashin hadin kai da banbance-banbancen addini a al’umma domin tabbatar da ci gaban Najeriya baki daya.
Ya yi bayanin cewa inganta rayuwar ma’aikata na daya daga cikin muhimman alkawuran da ya yi lokacin da yake yakin neman zabe, ya kuma bayar da tabbacin daukar matakai domin ganin ya cika wannan alkawari.
Tinubu ya nemi hadin kan dukkan ‘yan Najeriya, domin a cewar sa, dole ne a dauki tsauraran matakai domin a tabbatar da ma’aikatan Najeriya sun sami walwala mai yawa.