Tun lokacin da ake fitar da ƙuri’un da kowa ya samu kafin a fara ƙirge aka fahimci cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi wa sauran gagarumin rata.
Ga yanda kowa daga cikin masu neman takara 14 ya samu yayin da aka kammala ƙirga ƙuri’u.
- Emeka Nwajuba – 1
- David Umahi – 38
- Tunde Bakare – 0
- Rotimi Amaechi – 316
- Ahmed Rufai Sani – 4
- Yemi Osinbajo – 235
- Rochas Okorocha – 0
- Yahaya Bello – 47
- Tien Jack Rich – 0
- Ogbonnaya Onu – 1
- Ahmed Lawan – 152
- Ben Ayade: 37
- Ikeobasi Mokelu: 0
- Asiwaju Ahmed Tinubu: 1271