A jiya Talata ne mai neman shugabancin Majalissar Wakilai a majalissa ta 10, Dan Majalissa, Muktar Betara, ya rufe kofa da Shugaban Kasa Mai Jiran Gado, Bola Ahmed Tinubu.
Betara wanda shine Dan Majalissar Wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Biu/Bayo/Shani da Kwaya Kusar daga Jihar Borno ya jima yana neman amincewar sauran ‘yan jam’iyyarsa da ‘yan majalissa masu jiran rantsuwa, tsofin ‘yan majalissa da sauran masu ruwa da tsaki a kan bukatarsa ta zamewa shugaban Majalissar Wakilai.
An samu bayanan ganawar Betara da Tinubu ne daga Ofishin Yakin Neman Zaben Betara da ke Abuja a yau Laraba.
“Ganawar Betara da Shugaban Kasa mai Jiran Gado daya ce daga cikin ganawa da yawa da yai a watanni uku da suka gabata domin shiryawa kaddamawar da za aiwa wakilan a watan Yuni mai zuwa.
“Betara wanda a yanzu haka shine shugaban Kwamatin Kasafin Kudi na Majalissar Wakilai, ya samu tarba mai kyau a wajen Shugaban Kasa mai Jiran Gado, inda suka dauki hotuna a karshe.
“Ziyarar ganawar Betara da Shugaban Kasa mai Jiran Gado ta faru ne a gidan Shugaban da ke Defence House a Abuja bayan dawowar Shugaban daga hutu da kuma aikin Umara a Kasar Saudiyya,” in ji ofishin yakin neman zaben Betara.
NAN