For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tinubu Ya Zaɓi Wani Ɗan Katsina A Matsayin Ɗan Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa A APC

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya zaɓi Alhaji Kabir Ibrahim Masari a matsayin wanda da zai mara masa baya a takarar Shugaban Ƙasa da yake yi.

Jaridar DAILY TRUST ta gano cewa, Tinubu ya zaɓi hakan ne domin Masari ya riƙe masa wajen saboda gudun ƙarewar wa’adin da Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa ta bayar na miƙa sunayen ƴan takara domin babban zaɓen shekarar 2023.

Majiyoyi daga ɓangaren Tinubu da Masari sun tabbatar wa da DAILY TRUST labarin a jiya Alhamis da daddare.

Ɗan Takarar Mataimakin Shugaban Ƙasar na APC dai ya fito ne daga garin Masari, wani ƙauye a Ƙaramar Hukumar Kafur da ke Jihar Katsina.

Ɗan’uwane ga Gwamnan Jihar Katsina mai ci, Aminu Bello Masari.

Ya taɓa zama Sakataren Walwala na Ƙasa na Jam’iyyar APC a lokacin shugabancin Kwamared Adams Oshiomole wanda ya mulki APC a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.

A lokacin mulkin Jam’iyyar PDP na Malam Umaru Musa Yar’adua, Kabiru Masari ya kasance ɗan Jam’iyyar PDP, inda ya fice bayan rasuwar Yar’adua a shekarar 2010 ya haɗe da tafiyar Muhammadu Buhari ta CPC a wancan lokacin.

Comments
Loading...