For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tinubu Zai Miƙa Sunayen Ministocinsa Ga Majalissa A Yau – Bamidele

Shugaban Masu Rinjaye a Majalissar Dattawa, Micheal Opeyemi Bamidele ya sanar da cewa, sunayen ministocin Tinubu da aka daɗe ana jira zasu je Majalissar Dattawa a yau Laraba.

Ya bayyana hakan ne a wajen taron murnar cikarsa shekaru 60 a duniya da kuma ƙaddamar da littafi a Abuja.

Bamidele ya ce, Shugaba Tinubu ne da kansa ya sanar da shi hakan, a lokacin da ya kira shi domin taya shi murnar ranar zagayowar haihuwarsa.

A Karanta Wannan: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Wanke Sule Lamido Da Ƴaƴansa

Ya ce, Shugaba Tinubu ya sanar da shi cewa, ba zai samu damar halartar bikin murnar ba, saboda matsin da ake samu kan ganin an gabatar da sunayen ministocin ga Majalissar Dattawa kafin cikar wa’adin da aka saka na kwanaki 60 bayan rantsuwa.

Wani mai temakawa Shugaban Ƙasa da ya nemi a ɓoye sunansa a wata tattaunawa da PUNCH ya ce, Shugaban Ƙasar ya ja gabatar da sunayen ministocin ne zuwa ƙarshen lokaci domin samun tsantsanewa da fitar da abin da zai fi alheri ga Najeriya.

Ya ce sunayen da za a gabatar ya ƙunshi sunayen ƙwararru da ingantattun ƴan siyasar da aka tabbatar da nagartarsu ba kawai ƴan siyasa ba.

Ya ƙara da cewa a sunayen ba a yi la’akari da batun siyasa ba, an duba mutanen da zasu yi aiki ne domin ci gaban Najeriya.

Har yanzu dai ba a tabbaci kan mutanen da ke cikin jerin sunayen ministocin duk kuwa da yaɗuwar wasu sunaye da ba su samo asali daga Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ba.

Comments
Loading...