For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

TSADAR MAI: Babu Wani Shirin Dawo Da Tallafin Mai A Najeriya, In Ji Fadar Shugaban Ƙasa

Babban Mai Temakawa Shugaban Ƙasa a Kan Harkokin Yaɗa Labari da Hulɗa da Jama’a. Tope Ajayi, ya ce, babu wani shirin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu take yi na dawo da tallafin man fetur.

Ajayi ya yi wannan bayani ne a yau Alhamis a shafinsa na X wanda a baya ake kira da Twitter da misalin ƙarfe 6:08 agogon Najeriya.

Ya rubuta cewar, babu wani shiri na dawo da duk wani kala na tallafi, sannan kuma babu wani yanayi da zai sa a goyi bayan duk wani tashin farashin a wannan lokacin.

KARANTA WANNAN: Ba Zata Canja Zani Ba, Gwmantin Tinubu Irin Ta Buhari Ce, Ƴan Najeriya Su Shirya Karɓar Ƙaddara

Ya ƙara da cewar, Shugaban Ƙasa Tinubu ya gamsu da cewar, bisa bayanan da yake samu, za a iya ci gaba da kasancewa kan farashin da ake kai a yanzu haka.

Wannan rubutu na Ajayi dai ya zo ne, biyo bayan labaran da suke cewa, an ɗan dawo da tallafin man fetur saboda ƙaruwar kuɗin shigo da shi wanda ya samo asali daga faɗuwar darajar naira.

Comments
Loading...