Tsagin Jam’iyyar APC a Kano karkashin tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya jadda cewa, idan har ba adalci da gaskiya aka dosa ba, ba za a samu zaman lafiya a jam’iyyar APC reshen jihar Kano ba.
A ranar 7 ga wannan watan ne dai, tsagin ya rubutawa uwar jam’iyyar APC ta kasa cewa, bai amince da tsarin samar da sasanton da aka gabatar ba.
A wata sabuwar wasikar da tsagin ya tura Babban Ofishin Jam’iyyar na Kasa mai dauke da kwanan watan 10 ga Fabarairu, 2022, tsagin ya nemi a bashi kado 55 cikin 100 na shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kano ciki har da Shugaban Jam’iyya a jihar.
Sabuwar wasikar dai ta samu sanya hannun Sanata Ibrahim Shekarau, Sanata Barau Jibrin, Dan Majalissar Wakilai, Tijjani Jobe, Dan Majalissar Wakilai Nasiru Gabasawa, Dan Majalissar Wakilai Haruna Dederi, Dan Majalissar Wakilai Sha’aban Sharada da kuma Shugaban Kungiyar Buhari Support Group, Shehu Dalhatu.
Tsagin ya kuma jadda cewa, duk wani yunkuri na samar da daidaito kan rikicin ba zai samu jagorancin gwamna ba saboda kasancewarsa daya daga cikin masu sabanin.
Sannan kuma tsagin, ya bukaci bangaren Gwamna Ganduje da ya janye dukkanin wata daukaka kara da yai, a matsayin wata ‘yar manuniya da za ta nunawa ‘yan jam’iyya cewa da gaske yana son a samar sasanton.
Sannan kuma tsagin ya nuna cewa zai cigaba da martaba niyyar shugabancin jam’iyyar na kasa kan kokarinsa na samar da daidaito a APCn jihar Kano.
Wasikar ta jadda cewa, tsagin yana tabbatar da tsayawarsa a kan:
“1. Muna nan a kan batunmu na bukatar kaso 55% na shugabancin jam’iyya da kuma Shugaban Jam’iyya na Jiha, sannan a bayar da kaso 45% na shugabancin jam’iyya ga bangaren gwamna ba tare da wata ja-in-ja ba.
“2. Duk wani kwamitin samar da daidaito ko tsarin samar da daidaito da za a samar ya zama bai samu shugabancin gwamna ba, saboda kasancewarsa wani bangare na rikicin.
“3. Tsarin cigaba da samar da sasanton zai tabbata ne idan har bangaren gwamna ya janye daukaka karar da ya shigar a kan rikicin a matsayin nuna gaskiyar da za ta kara mana karfin guiwa.
A karshe, tsagin Shekarau ya bukaci shugabancin jam’iyyar na kasa da yai duk mai yiwuwa wajen kawo karshen rikicin gida a APCn jihar Kano.
(PUNCH)