Tsagin jam’iyyar APC a jihar Kano wanda ake kira da G-7 ya yi watsi da takardar samar da daidaito a jam’iyyar APC reshen jihar Kano wadda take fama da rikici.
A cikin wasikar da Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC ta gabatar ga reshen jam’iyyar na Kano wadda aka turawa gwamnan Kano Ganduje, an gabatar da tsare-tsaren yanda za a samar da daidaito game da rikicin da ya addabi jam’iyyar.
To sai dai kuma tsagin G-7 da Shekarau ke jagoranta ya yi watsi da takardar inda ya ce, “ba mu yarda da kafatanin bayanan da suke cikin wasikarku ba.”
Wannan na kunshe ne cikin takardar da akaiwa take da “Re: Guidelines for the Harmonization of the Party Structure in Kano”.
Cikin dalilan da suka fada a takardar akwai cewa, takardar ba ta kunshi abubuwan da bangarori biyu suka gabatar a zaman sulhun da akai da dama a baya ba.
Sannan sun yi korafin cewa, takardar ta yadu a kafafen sadarwar zamani kafin ta iso garesu.
“Mun yi tunanin bayanan da za ku bayar za su kunshi bukatun da aka gabatar muku ne.
“Abin takaici, haka kuma, takardar ku ba ta kunshi bukatun da aka gabatar gareku ba daga ɓangarorin biyu, ba ma ko a kawo su a matsayin hujjar samar da wannan ba,” wani sashin na takardar ya ce.