For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tsagin Ganduje Ya Kayar Da Tsagin Shekarau A Kotun Daukaka Kara

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin Babbar Kotun Abuja wadda ta tabbatar da ingancin zaben shugabancin APC na tsagin Shekarau.

Da take tabbatar da hukuncin watsi da hukuncin Babbar Kotun, Kotun Daukaka Karar ta baiyana cewa, waccan kotun ba ta da hurumin saurarar karar.

Kotun ta ce, karar ba ta shafi karar kafin zabe ba, inda ta kara da cewa karar ta shafi rikicin cikin gidan jam’iyya ne.

Lauyan Tsagin Shekarau, Nureini Jimoh SAN, ya ce, abun mamakine matuka kan cewa sun rasa nasara a duk kararrakin.

Ya baiyanawa jaridar DAILY NIGERIAN cewa za su daukaka kara zuwa Kotun Koli domin su kalubalanci hukuncin.

(DAILY NIGERIAN)

Comments
Loading...