For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tsagin Shekarau Da Tsagin Ganduje Duk Suna Son A Basu Takarar Gwamnan Kano

Kwamitin sasanto kan rikicin jam’iyyar APC a Kano, zai a cigaba da zaman sasanton gobe, yayinda kwamitin ke gabatar da tsarin raba dai-dai na shugabancin jam’iyyar ga bangarori masu rigima da juna a jihar.

Wani daga cikin masu zaman wanda ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa, bangaren Shekarau sun bukaci a basu lokaci domin tattaunawa kan abubuwan da aka gabatar musu kafin su yanke hukunci.

Dukkanin bangarorin biyu sun bukaci a bar musu mukamin shugaban jam’iyya da kuma damar fitar da dan-takarar gwamnan jihar a matsayin wasu daga cikin sharudan sasanton.

Shugaban Kwamitin Riko na APC a kasa, Mai Mala Buni shine ya jagoranci zaman a Abuja, kuma a tare da shi akawai gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar da ma wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

KU KARANTA: Amaechi Zai Iya Zama Zabin Buhari A 2023

Tattaunawar na daya daga cikin kokarin jam’iyyar na sasanta ‘ya’yanta da suka samu sabani kafin zuwan Babban Taron Jam’iyyar na kasa.

Kwaminitin Buni na nufin magance rikice-rikicen jam’iyyar domin samun damar gudanar da lafiyayyen Babban Taron jam’iyyar.

A baya dai, lokacin zaben shugabannin jam’iyyar reshen jihohi, bangaren Gwamna Ganduje da na Shekarau sun gabatar da mabambantan tarurrukan zaben shegabannin jam’iyyar a jihar Kano.

Hakan kuma ya haifar da shugabannin jam’iyyar bangare biyu wadanda suke cigaba da samun sabani da juna.

(Sahelian Times)

Comments
Loading...