For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

APCn KANO: Tsagin Shekarau Za Su Fitar Da Matsaya, Yayin Da Tsagin Ganduje Ke Kiran A Hada Kai

‘Yan awanni kadan bayan samun nasarar da tsagin APC da ke yiwa Gwamna Gaduje ya yi a Kotun Daukaka Kara, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kiran neman samun hadin kai ga tsagin abokin hamaiyarsa, Malam Ibrahim Shekarau.

Da yake magana da DAILY TRUST kan hukuncin Kotun Daukaka Karar na yau, Gwamna Ganduje ya ce, da ma yana da yakinin cewa gaskiya za tai halinta, saboda haka yana murna da hukuncin.

Gwamnan ya yi maganar ne ta bakin Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, inda ya kara da cewa, hukuncin zai kara hada kan jam’iyyar APC a jihar Kano.

Ya ce, yana fatan Malam Ibrahim Shekarau da sauran ‘yan G7 masu hamaiya da tsaginsa za su aminta da hukuncin kotun, “su zo mu tafi tare mu ga yanda zamu tsara jam’iyyarmu ta yanda za mu samu nasara a zabubbukan 2023.

“Wannan lokaci ne mai muhimmanci ga kowanne dan jam’iyya domin a hadu tare a yi aiki tare wajen hadin kai da cigaban jam’iyya,” in ji Ganduje.

A daren yau ne, tsagin Shekarau na G7 zai zauna domin duba hukuncin kotun tare da daukar matsaya kan abu na gaba da tsagin zai yi.

Wani daga cikin ‘yan tsagin G7, ya fadawa DAILY TRUST cewa, sai bayan zaman ne, tsagin zai baiyana matsayarsa game da hukuncin kotun.

Sai dai kuma an rawaito cewa, bayan baiyana hukuncin kotun daukaka karar na yau, lauyan tsagin Shekarau, Nureini Jimoh ya baiyana mamakinsa game da rashin nasararsu a kotun, inda ya ce za su nufi Kotun Koli.

Comments
Loading...