For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tsarin Da ASUU Ta Gabatar Na Biyan Albashi Ya Gaza Tsallake Gwaji

Gwamnatin Tarayya ta ce tsarin biyan albashi na Universities Transparency Accountability Solution, UTAS, wanda Kungiyar ASUU ta gabatar ya gaza tsallake gwajin tabbatar da ingancin da akai.

Wannan gazawa dai ta nuna cewa malaman jami’ar ba za su bar kan tsarin Integrated Payroll and Personnel Information System, IPPIS ba wanda suke zargin rashin dacewa da tsarin aikinsu.

Kungiyar ASUU dai ta dade tana kalubalantar tsarin IPPIS, abinda ya sa ta kirkiro tsarin UTAS wanda take ganin ya fi dacewa da tsarin aikin malaman jami’ar.

A lokacin gabatar da tsarin UTAS, kungiyar ASUU ta bugi kirjin cewa, tsarin UTAS ya fi IPPIS inganci da kuma dacewa musamman kasancewarsa tsarin da masana ‘yan asalin Najeriya suka samar sabanin IPPIS wanda akai kwangilarsa a kasar waje.

Wannan rikita-rikitar dai na daya daga cikin sabanin da yake kara ta’azzara rigimar da ke tsakanin kungiyar ASUU da Gwamnatin Tarayya.

Za dai a kara tantance UTAS a wannan wata da muke ciki.

Comments
Loading...