For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tsarin Samar Da Sukari Zai Iya Samawa Najeriya Dala Miliyan 700 Kowacce Shekara – Dangote

Shugaban kamfanin sukari na Dangote Sugar Refinery Plc, Aliko Dangote ya ce, idan aka aiwatar da tsarin samar da sukari na kasa (NSMP), yadda aka tsara, zai iya ceton kudaden musaya na kasashen waje sama da dala miliyan 700 a duk shekara.

Dangote, a cewar wata sanarwa daga kamfanin, ya bayyana hakan ne yayin rangadin kayan aiki da wasu ‘yan kasuwa suka yi ranar Litinin a Legas.

Ya kuma yi gargadin cewa dole ne a kare tsarin don temakawa tattalin arzikin Najeriya don a cimma tagwayen manufofi na samar da masana’antu da kuma samar da ayyukan yi.

“Idan aka bi tsarin samar da sukari na kasa sosai kuma masu aiki duk suka bi ka’idoji, kasar za ta kara samun cigaba, saboda Najeriya za ta samu damar adana tsakanin dala miliyan 600 zuwa dala miliyan 700 a shekara a matsayin musayar kasashen waje,” in ji shi.

Dangote ya kuma shaidawa masu ziyarar cewa rukunin kamfanoni na Dangote na kara kaimi kan ayyukan jin kai ga al’ummomin da ke saukar bakuncin kamfanoninsa a fadin kasar.

Ya ce ana kokarin samar da tagomashi mai kyau ga al’ummomin da ke saukar bakuncin, saboda a kan hakan kamfanoninsa sun kashe biliyoyin nairori a jihohin da wadannan kamfanoni suka kasance.

Dangote ya ce, irin wadannan ayyukan ba sa cikin irin aiyukan da gidauniyarsa ta Aliko Dangote Foundation ke aiwatarwa.

Ya ce a yanzu haka gidauniyar tana bayar da tallafi ga mata masu rauni a cikin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar nan.

Babban Manajan shirin samar da sukari a kamfanin Dangote, John Beverley, ya ce lokacin da masana’antar ta fara aiki sosai, za ta sami karfin amfani da tan 12,000 na rake a kowacce rana.

Ya ce za a samar da wutar lantarki ta megawat 90 don amfanin kamfanin da kuma al’ummomin da ke makwabtaka da kamfanin.

(NAN)

Comments
Loading...