For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Tsawon Shekaru 14 Ba A Yiwa Malaman Firamare Promotion Ba A Adamawa

Shugaban Hukumar Ilimi a Matakin Farko (SUBEB), Salihi Ateequ, ya baiyana cewa babu malamin firamare ko daya da aka ciyar gaba a jihar cikin tsawon shekaru 14 da suka gabata.

Salihi Ateequ ya baiyana hakan ne jiya Litinin a Yola, inda ya kara da cewa har yanzu ana biyan malaman makaranta tsohon tsarin albashi ne na naira 18,000 maimakon naira 32,000.

“Malaman makarantun firamare a jihar nan ba a ciyar da su gaba ba tsawon shekaru 14 da suka wuce, kuma abun babu dadi,” in ji shi.

Shugaban na SUBEB ya ce, hukumar tana tattaunawa da gwamnatin gwamna mai ci a jihar, Ahmadu Fintiri kan samar da mafita.

“Hukumar ta zauna, ta duba yanayin inda a karshe ta yanke hukuncin baiwa gwamnati shawara kan yanda za a shawo kai tare da magance wannan mummunar matsala.

“Mun dauki bayanan duk wadanda suka cancanci a ciyar da su gaba cikin shekaru 14 da suka gabata; mun gano cewa kudin da ake bi ya girmama sosai.

“Kudin ya kai wajen naira miliyan 300, kuma wadannan kudade ba sun taru ba ne a iya lokacin wannan gwamnatin ba,” in ji shugaban.

Ya kuma baiyana cewa, hukumar ta SUBEB ta baiwa gwamnati shawarar biyan kudeden a hankali a hankali domin samun saukin sauke nauyin.

Ya ce an baiwa gwamnati shawarar da su biya na shekaru 4 a lokaci guda, da kuma wasu shekaru 4n, inda ya kara da cewa “cikin dan lokaci kadan sai a gama biyan kudaden.”

Comments
Loading...