Tsohon mataimakin gwamna a jihar Gombe, Mista John Yoriyo tare da wasu jigajigan jam’iyyar APC mai Mulki a jihar sun koma jam’iyyar PDP.
An karbi tsohon mataimakin gwamnan tare da magoya bayansa jiya Asabar a Gombe a taron karbar da shugaban PDP na jihar Manjo Janar (mai ritaya) Abnor Kwaskebe ya jagoranta.
Da yake jawabi a wajen taron, Yoriyo, tsohon mataimakin tsohon gwamnan jihar Danjuma Goje, ya kalubalanci irin jagorancin da jam’iyyar APC ta ke a jihar, inda ya bayyana PDP a matsayin jam’iyyar da ta fi dacewa.
“A bayyane yake cewa jam’iyyar APC ta gaza a Najeriya, musamman a bangaren tsaro,” in ji shi.
“Da ina cikin APC, kuma na ga duk abubuwan da suke faruwa, babu wani abun burgewa. PDP nan ne wajen da ya fi dacewa a kasance.”
Ya kara da cewa “Babu wani abu da yai kama da demokaradiya a karkashin mulkin APC a Gombe, babu wanda ya san me ke faruwa, an rufe mana komai, kawai mulkar me ake yi.”
Da yake na sa jawabin, Kwaskebe, shugaban PDP na jihar Gombe, ya bayyana cewa jigajigan APCn sun dawo gida ne.
“Muna farincikin karbar wadanda suka bar jam’iyyarmu suna tunanin PDP ta rushe. Yanzu kam suna dawowa gida,” in ji shi.